محمد   سورة  : Muhammad


سورة Sura   محمد   Muhammad
وَيَقُولُ الَّذِينَ آمَنُوا لَوْلَا نُزِّلَتْ سُورَةٌ ۖ فَإِذَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ مُّحْكَمَةٌ وَذُكِرَ فِيهَا الْقِتَالُ ۙ رَأَيْتَ الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ نَظَرَ الْمَغْشِيِّ عَلَيْهِ مِنَ الْمَوْتِ ۖ فَأَوْلَىٰ لَهُمْ (20) طَاعَةٌ وَقَوْلٌ مَّعْرُوفٌ ۚ فَإِذَا عَزَمَ الْأَمْرُ فَلَوْ صَدَقُوا اللَّهَ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ (21) فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوا أَرْحَامَكُمْ (22) أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَعَنَهُمُ اللَّهُ فَأَصَمَّهُمْ وَأَعْمَىٰ أَبْصَارَهُمْ (23) أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ الْقُرْآنَ أَمْ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقْفَالُهَا (24) إِنَّ الَّذِينَ ارْتَدُّوا عَلَىٰ أَدْبَارِهِم مِّن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ الْهُدَى ۙ الشَّيْطَانُ سَوَّلَ لَهُمْ وَأَمْلَىٰ لَهُمْ (25) ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا لِلَّذِينَ كَرِهُوا مَا نَزَّلَ اللَّهُ سَنُطِيعُكُمْ فِي بَعْضِ الْأَمْرِ ۖ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِسْرَارَهُمْ (26) فَكَيْفَ إِذَا تَوَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ يَضْرِبُونَ وُجُوهَهُمْ وَأَدْبَارَهُمْ (27) ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ اتَّبَعُوا مَا أَسْخَطَ اللَّهَ وَكَرِهُوا رِضْوَانَهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَالَهُمْ (28) أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخْرِجَ اللَّهُ أَضْغَانَهُمْ (29)
الصفحة Page 509
(20) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
(21) Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu, to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.
(22) To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke zumuntarku?
(23) Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu.
(24) Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?
(25) lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta musu (haka), kuma ya yi musu shibta.
(26) Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.
(27) To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?
(28) Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu.
(29) Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022