الأعلى   سورة  : Al-A'laa


سورة Sura   الأعلى   Al-A'laa
الطارق At-Taariq
وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ (1) وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ (2) النَّجْمُ الثَّاقِبُ (3) إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ (4) فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ (5) خُلِقَ مِن مَّاءٍ دَافِقٍ (6) يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ (7) إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ (8) يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ (9) فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ (10) وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ (11) وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ (12) إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ (13) وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ (14) إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا (15) وَأَكِيدُ كَيْدًا (16) فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا (17)
الأعلى Al-A'laa
سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى (1) الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ (2) وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ (3) وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَىٰ (4) فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَىٰ (5) سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰ (6) إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ (7) وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ (8) فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَىٰ (9) سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ (10) وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى (11) الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَىٰ (12) ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ (13) قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ (14) وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّىٰ (15)
الصفحة Page 591
الطارق At-Taariq
(1) Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
(2) To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
(3) Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
(4) Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
(5) To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
(6) An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
(7) Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
(8) Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
(9) Rãnar da ake jarrabawar asirai.
(10) Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
(11) Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
(12) Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
(13) Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
(14) Kuma shĩ bã bananci bane
(15) Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
(16) Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
(17) Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
الأعلى Al-A'laa
(1) Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
(2) Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
(3) Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
(4) Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
(5) Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
(6) Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
(7) Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
(8) Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
(9) Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
(10) Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
(11) Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
(12) Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
(13) Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
(14) Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
(15) Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022