(160) Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
(161) A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
(162) "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
(163) "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
(164) "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
(165) "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
(166) "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
(167) Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
(168) Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
(169) "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
(170) Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.
(171) Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
(172) Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu.
(173) Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
(174) Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.
(175) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
(176) Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
(177) A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
(178) "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
(179) "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
(180) "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
(181) "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
(182) "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
(183) "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."