الأحزاب   سورة  : Al-Ahzaab


سورة Sura   الأحزاب   Al-Ahzaab
يَسْأَلُكَ النَّاسُ عَنِ السَّاعَةِ ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللَّهِ ۚ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا (63) إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرًا (64) خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (65) يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَا (66) وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَا (67) رَبَّنَا آتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنًا كَبِيرًا (68) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ آذَوْا مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ اللَّهُ مِمَّا قَالُوا ۚ وَكَانَ عِندَ اللَّهِ وَجِيهًا (69) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا (70) يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ ۗ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا (71) إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَن يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنسَانُ ۖ إِنَّهُ كَانَ ظَلُومًا جَهُولًا (72) لِّيُعَذِّبَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ وَيَتُوبَ اللَّهُ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا (73)
الصفحة Page 427
(63) Sunã tambayar ka ga Sã'a. Ka ce: "Saninta yanã wurin Allah kawai." Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa?
(64) Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna.
(65) Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki.
(66) Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, "Kaitonmu, sabõda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!"
(67) Kuma suka ce: "Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya!
(68) "Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma."
(69) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.
(70) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya.
(71) Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma.
(72) Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci.
(73) Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022