(176) Sunã yi maka fatawa. Ka ce: "Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.
المائدة Al-Maaida
(1) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.
(2) Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.