الحجر   سورة  : Al-Hijr


سورة Sura   الحجر   Al-Hijr
قَالَ هَٰؤُلَاءِ بَنَاتِي إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ (71) لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِي سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ (72) فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ (73) فَجَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ (74) إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّلْمُتَوَسِّمِينَ (75) وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٍ مُّقِيمٍ (76) إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ (77) وَإِن كَانَ أَصْحَابُ الْأَيْكَةِ لَظَالِمِينَ (78) فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٍ مُّبِينٍ (79) وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَابُ الْحِجْرِ الْمُرْسَلِينَ (80) وَآتَيْنَاهُمْ آيَاتِنَا فَكَانُوا عَنْهَا مُعْرِضِينَ (81) وَكَانُوا يَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا آمِنِينَ (82) فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ (83) فَمَا أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ (84) وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ ۗ وَإِنَّ السَّاعَةَ لَآتِيَةٌ ۖ فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ (85) إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْخَلَّاقُ الْعَلِيمُ (86) وَلَقَدْ آتَيْنَاكَ سَبْعًا مِّنَ الْمَثَانِي وَالْقُرْآنَ الْعَظِيمَ (87) لَا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعْنَا بِهِ أَزْوَاجًا مِّنْهُمْ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ (88) وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذِيرُ الْمُبِينُ (89) كَمَا أَنزَلْنَا عَلَى الْمُقْتَسِمِينَ (90)
الصفحة Page 266
(71) Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
(72) Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
(73) Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
(74) Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
(75) Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
(76) Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.
(77) Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
(78) Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
(79) Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
(80) Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.
(81) Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
(82) Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
(83) Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
(84) Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
(85) Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
(86) Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
(87) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma.
(88) Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
(89) Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."
(90) Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022