(52) A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
(53) Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."
(54) Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
(55) Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
(56) Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"
(57) Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"
(58) Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
(59) "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
(60) "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
(61) To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
(62) Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
(63) Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
(64) "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
(65) "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
(66) Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
(67) Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
(68) Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
(69) "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
(70) Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"