الرحمن   سورة  : Ar-Rahmaan


سورة Sura   الرحمن   Ar-Rahmaan
يُعْرَفُ الْمُجْرِمُونَ بِسِيمَاهُمْ فَيُؤْخَذُ بِالنَّوَاصِي وَالْأَقْدَامِ (41) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (42) هَٰذِهِ جَهَنَّمُ الَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا الْمُجْرِمُونَ (43) يَطُوفُونَ بَيْنَهَا وَبَيْنَ حَمِيمٍ آنٍ (44) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (45) وَلِمَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ جَنَّتَانِ (46) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (47) ذَوَاتَا أَفْنَانٍ (48) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (49) فِيهِمَا عَيْنَانِ تَجْرِيَانِ (50) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (51) فِيهِمَا مِن كُلِّ فَاكِهَةٍ زَوْجَانِ (52) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (53) مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ فُرُشٍ بَطَائِنُهَا مِنْ إِسْتَبْرَقٍ ۚ وَجَنَى الْجَنَّتَيْنِ دَانٍ (54) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (55) فِيهِنَّ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَانٌّ (56) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (57) كَأَنَّهُنَّ الْيَاقُوتُ وَالْمَرْجَانُ (58) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (59) هَلْ جَزَاءُ الْإِحْسَانِ إِلَّا الْإِحْسَانُ (60) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (61) وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ (62) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (63) مُدْهَامَّتَانِ (64) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (65) فِيهِمَا عَيْنَانِ نَضَّاخَتَانِ (66) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (67)
الصفحة Page 533
(41) zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
(42) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(43) Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
(44) Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
(45) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(46) Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
(47) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(48) Mãsu rassan itãce.
(49) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(50) A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
(51) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(52) A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.
(53) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(54) Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
(55) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(56) A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
(57) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(58) Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
(59) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(60) Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.
(61) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(62) Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
(63) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(64) Mãsu duhun inuwa.
(65) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(66) A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
(67) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022