(62) Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai.
(63) Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(64) Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai.
(65) Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta.
(66) A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.
(67) Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(68) Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta, dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.
(69) Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.