السجدة   سورة  : As-Sajda


سورة Sura   السجدة   As-Sajda
وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الْمُجْرِمُونَ نَاكِسُو رُءُوسِهِمْ عِندَ رَبِّهِمْ رَبَّنَا أَبْصَرْنَا وَسَمِعْنَا فَارْجِعْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ (12) وَلَوْ شِئْنَا لَآتَيْنَا كُلَّ نَفْسٍ هُدَاهَا وَلَٰكِنْ حَقَّ الْقَوْلُ مِنِّي لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ (13) فَذُوقُوا بِمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا إِنَّا نَسِينَاكُمْ ۖ وَذُوقُوا عَذَابَ الْخُلْدِ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (14) إِنَّمَا يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا الَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِهَا خَرُّوا سُجَّدًا وَسَبَّحُوا بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ ۩ (15) تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ (16) فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَّا أُخْفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (17) أَفَمَن كَانَ مُؤْمِنًا كَمَن كَانَ فَاسِقًا ۚ لَّا يَسْتَوُونَ (18) أَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ جَنَّاتُ الْمَأْوَىٰ نُزُلًا بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (19) وَأَمَّا الَّذِينَ فَسَقُوا فَمَأْوَاهُمُ النَّارُ ۖ كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا وَقِيلَ لَهُمْ ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (20)
الصفحة Page 416
(12) Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne."
(13) Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya.
(14) To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
(15) Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai.
(16) Sãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su.
(17) Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(18) Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba.
(19) Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(20) Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022