الانسان   سورة  : Al-Insaan


سورة Sura   الانسان   Al-Insaan
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ (20) وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ (21) وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ (22) إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ (23) وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ (24) تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ (25) كَلَّا إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِيَ (26) وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ (27) وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ (28) وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ (29) إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ (30) فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ (31) وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (32) ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰ أَهْلِهِ يَتَمَطَّىٰ (33) أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ (34) ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ (35) أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَن يُتْرَكَ سُدًى (36) أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمْنَىٰ (37) ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ (38) فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ (39) أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن يُحْيِيَ الْمَوْتَىٰ (40)
الانسان Al-Insaan
هَلْ أَتَىٰ عَلَى الْإِنسَانِ حِينٌ مِّنَ الدَّهْرِ لَمْ يَكُن شَيْئًا مَّذْكُورًا (1) إِنَّا خَلَقْنَا الْإِنسَانَ مِن نُّطْفَةٍ أَمْشَاجٍ نَّبْتَلِيهِ فَجَعَلْنَاهُ سَمِيعًا بَصِيرًا (2) إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا (3) إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ سَلَاسِلَ وَأَغْلَالًا وَسَعِيرًا (4) إِنَّ الْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِن كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا (5)
الصفحة Page 578
(20) A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
(21) Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
(22) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
(23) Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
(24) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
(25) Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
(26) A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
(27) kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
(28) Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
(29) Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
(30) Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
(31) To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
(32) Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
(33) Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
(34) Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
(35) Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
(36) Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
(37) Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
(38) Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
(39) Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
(40) Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?
الانسان Al-Insaan
(1) Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
(2) Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
(3) Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
(4) Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
(5) Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022