البلد   سورة  : Al-Balad


سورة Sura   البلد   Al-Balad
يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي (24) فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُ أَحَدٌ (25) وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُ أَحَدٌ (26) يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ (27) ارْجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً (28) فَادْخُلِي فِي عِبَادِي (29) وَادْخُلِي جَنَّتِي (30)
البلد Al-Balad
لَا أُقْسِمُ بِهَٰذَا الْبَلَدِ (1) وَأَنتَ حِلٌّ بِهَٰذَا الْبَلَدِ (2) وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ (3) لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي كَبَدٍ (4) أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ (5) يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا (6) أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُ أَحَدٌ (7) أَلَمْ نَجْعَل لَّهُ عَيْنَيْنِ (8) وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ (9) وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ (10) فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ (11) وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ (12) فَكُّ رَقَبَةٍ (13) أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ (14) يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ (15) أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ (16) ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ (17) أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ (18) وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ (19) عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌ (20)
الصفحة Page 594
(24) Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"
(25) To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
(26) Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
(27) Yã kai rai mai natsuwa!
(28) Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
(29) Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
(30) Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).
البلد Al-Balad
(1) Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.
(2) Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
(3) Da mahaifi da abin da ya haifa.
(4) Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
(5) Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
(6) Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa,"
(7) Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
(8) Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
(9) Da harshe, da leɓɓa biyu.
(10) Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba?
(11) To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
(12) Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
(13) Ita ce fansar wuyan bãwa.
(14) Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
(15) Ga marãya ma'abũcin zumunta.
(16) Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
(17) Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
(18) Waɗannan ne ma'abũta albarka
(19) Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci
(20) A kansu akwai wata wuta abar kullewa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022