الرحمن   سورة  : Ar-Rahmaan


سورة Sura   الرحمن   Ar-Rahmaan
فِيهِمَا فَاكِهَةٌ وَنَخْلٌ وَرُمَّانٌ (68) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (69) فِيهِنَّ خَيْرَاتٌ حِسَانٌ (70) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (71) حُورٌ مَّقْصُورَاتٌ فِي الْخِيَامِ (72) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (73) لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَانٌّ (74) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (75) مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ رَفْرَفٍ خُضْرٍ وَعَبْقَرِيٍّ حِسَانٍ (76) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (77) تَبَارَكَ اسْمُ رَبِّكَ ذِي الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ (78)
الواقعة Al-Waaqia
إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ (1) لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ (2) خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ (3) إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّا (4) وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّا (5) فَكَانَتْ هَبَاءً مُّنبَثًّا (6) وَكُنتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةً (7) فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ (8) وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ (9) وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَ (10) أُولَٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَ (11) فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ (12) ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ (13) وَقَلِيلٌ مِّنَ الْآخِرِينَ (14) عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ (15) مُّتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَ (16)
الصفحة Page 534
(68) A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
(69) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(70) A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
(71) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(72) Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
(73) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(74) Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
(75) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(76) Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
(77) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(78) Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.
الواقعة Al-Waaqia
(1) Idan mai aukuwa ta auku.
(2) Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
(3) (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
(4) Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
(5) Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
(6) Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
(7) Kuma kun kasance nau'i uku.
(8) Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
(9) Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
(10) Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
(11) Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
(12) A ckin Aljannar ni'ima.
(13) Jama'a ne daga mutãnen farko.
(14) Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
(15) (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
(16) Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022