الأعراف   سورة  : Al-A'raaf


سورة Sura   الأعراف   Al-A'raaf
وَلَقَدْ جِئْنَاهُم بِكِتَابٍ فَصَّلْنَاهُ عَلَىٰ عِلْمٍ هُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ (52) هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأْوِيلَهُ ۚ يَوْمَ يَأْتِي تَأْوِيلُهُ يَقُولُ الَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبْلُ قَدْ جَاءَتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَاءَ فَيَشْفَعُوا لَنَا أَوْ نُرَدُّ فَنَعْمَلَ غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ ۚ قَدْ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ (53) إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ ۗ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ ۗ تَبَارَكَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ (54) ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ (55) وَلَا تُفْسِدُوا فِي الْأَرْضِ بَعْدَ إِصْلَاحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفًا وَطَمَعًا ۚ إِنَّ رَحْمَتَ اللَّهِ قَرِيبٌ مِّنَ الْمُحْسِنِينَ (56) وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَقَلَّتْ سَحَابًا ثِقَالًا سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاءَ فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۚ كَذَٰلِكَ نُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ (57)
الصفحة Page 157
(52) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani.
(53) Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu.
(54) Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!
(55) Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka.
(56) Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa.
(57) Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022