القيامة   سورة  : Al-Qiyaama


سورة Sura   القيامة   Al-Qiyaama
فَمَا تَنفَعُهُمْ شَفَاعَةُ الشَّافِعِينَ (48) فَمَا لَهُمْ عَنِ التَّذْكِرَةِ مُعْرِضِينَ (49) كَأَنَّهُمْ حُمُرٌ مُّسْتَنفِرَةٌ (50) فَرَّتْ مِن قَسْوَرَةٍ (51) بَلْ يُرِيدُ كُلُّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُؤْتَىٰ صُحُفًا مُّنَشَّرَةً (52) كَلَّا ۖ بَل لَّا يَخَافُونَ الْآخِرَةَ (53) كَلَّا إِنَّهُ تَذْكِرَةٌ (54) فَمَن شَاءَ ذَكَرَهُ (55) وَمَا يَذْكُرُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ ۚ هُوَ أَهْلُ التَّقْوَىٰ وَأَهْلُ الْمَغْفِرَةِ (56)
القيامة Al-Qiyaama
لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ (1) وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ (2) أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ (3) بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ (4) بَلْ يُرِيدُ الْإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ (5) يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ (6) فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ (7) وَخَسَفَ الْقَمَرُ (8) وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ (9) يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ (10) كَلَّا لَا وَزَرَ (11) إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ (12) يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ (13) بَلِ الْإِنسَانُ عَلَىٰ نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ (14) وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُ (15) لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ (16) إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ (17) فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ (18) ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ (19)
الصفحة Page 577
(48) Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
(49) Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
(50) Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
(51) Sun gudu daga zãki.
(52) A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
(53) A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
(54) A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
(55) Dõmin wanda ya so, ya tuna.
(56) Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.
القيامة Al-Qiyaama
(1) Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
(2) Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
(3) Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
(4) Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
(5) Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
(6) Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
(7) To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
(8) Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
(9) Aka tãra rãnã da watã
(10) Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
(11) A'aha! bãbu mafaka.
(12) zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
(13) Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
(14) Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
(15) Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
(16) Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
(17) Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
(18) To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
(19) sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022