المدثر   سورة  : Al-Muddaththir


سورة Sura   المدثر   Al-Muddaththir
۞ إِنَّ رَبَّكَ يَعْلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدْنَىٰ مِن ثُلُثَيِ اللَّيْلِ وَنِصْفَهُ وَثُلُثَهُ وَطَائِفَةٌ مِّنَ الَّذِينَ مَعَكَ ۚ وَاللَّهُ يُقَدِّرُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ ۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحْصُوهُ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۖ فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنَ الْقُرْآنِ ۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرْضَىٰ ۙ وَآخَرُونَ يَضْرِبُونَ فِي الْأَرْضِ يَبْتَغُونَ مِن فَضْلِ اللَّهِ ۙ وَآخَرُونَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۖ فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنْهُ ۚ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَقْرِضُوا اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللَّهِ هُوَ خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا ۚ وَاسْتَغْفِرُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (20)
المدثر Al-Muddaththir
يَا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ (1) قُمْ فَأَنذِرْ (2) وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ (3) وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ (4) وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ (5) وَلَا تَمْنُن تَسْتَكْثِرُ (6) وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْ (7) فَإِذَا نُقِرَ فِي النَّاقُورِ (8) فَذَٰلِكَ يَوْمَئِذٍ يَوْمٌ عَسِيرٌ (9) عَلَى الْكَافِرِينَ غَيْرُ يَسِيرٍ (10) ذَرْنِي وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدًا (11) وَجَعَلْتُ لَهُ مَالًا مَّمْدُودًا (12) وَبَنِينَ شُهُودًا (13) وَمَهَّدتُّ لَهُ تَمْهِيدًا (14) ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَ (15) كَلَّا ۖ إِنَّهُ كَانَ لِآيَاتِنَا عَنِيدًا (16) سَأُرْهِقُهُ صَعُودًا (17)
الصفحة Page 575
(20) Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
المدثر Al-Muddaththir
(1) Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
(2) Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
(3) Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
(4) Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
(5) Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
(6) Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
(7) Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
(8) To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
(9) To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
(10) A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
(11) Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
(12) Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
(13) Da ɗiyã halartattu,
(14) Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
(15) Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
(16) Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
(17) Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022