الفجر   سورة  : Al-Fajr


سورة Sura   الفجر   Al-Fajr
الفجر Al-Fajr
وَالْفَجْرِ (1) وَلَيَالٍ عَشْرٍ (2) وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ (3) وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ (4) هَلْ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجْرٍ (5) أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ (6) إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ (7) الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلَادِ (8) وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ (9) وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ (10) الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ (11) فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ (12) فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ (13) إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ (14) فَأَمَّا الْإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ (15) وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ (16) كَلَّا ۖ بَل لَّا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ (17) وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ الْمِسْكِينِ (18) وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا (19) وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا (20) كَلَّا إِذَا دُكَّتِ الْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا (21) وَجَاءَ رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا (22) وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّىٰ لَهُ الذِّكْرَىٰ (23)
الصفحة Page 593
الفجر Al-Fajr
(1) Inã rantsuwa da alfijiri.
(2) Da darũruwa gõma.
(3) Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.
(4) Da dare idan yana shũɗewa.
(5) Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
(6) Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
(7) Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.
(8) Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
(9) Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?
(10) Da Fir'auna mai turãku.
(11) Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
(12) Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
(13) Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
(14) Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
(15) To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."
(16) Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."
(17) A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
(18) Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
(19) Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
(20) Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
(21) A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
(22) Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.
(23) Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022