غافر   سورة  : Ghafir


سورة Sura   غافر   Ghafir
وَلَقَدْ جَاءَكُمْ يُوسُفُ مِن قَبْلُ بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا زِلْتُمْ فِي شَكٍّ مِّمَّا جَاءَكُم بِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا هَلَكَ قُلْتُمْ لَن يَبْعَثَ اللَّهُ مِن بَعْدِهِ رَسُولًا ۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ اللَّهُ مَنْ هُوَ مُسْرِفٌ مُّرْتَابٌ (34) الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِ اللَّهِ بِغَيْرِ سُلْطَانٍ أَتَاهُمْ ۖ كَبُرَ مَقْتًا عِندَ اللَّهِ وَعِندَ الَّذِينَ آمَنُوا ۚ كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلْبِ مُتَكَبِّرٍ جَبَّارٍ (35) وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا هَامَانُ ابْنِ لِي صَرْحًا لَّعَلِّي أَبْلُغُ الْأَسْبَابَ (36) أَسْبَابَ السَّمَاوَاتِ فَأَطَّلِعَ إِلَىٰ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُ كَاذِبًا ۚ وَكَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِفِرْعَوْنَ سُوءُ عَمَلِهِ وَصُدَّ عَنِ السَّبِيلِ ۚ وَمَا كَيْدُ فِرْعَوْنَ إِلَّا فِي تَبَابٍ (37) وَقَالَ الَّذِي آمَنَ يَا قَوْمِ اتَّبِعُونِ أَهْدِكُمْ سَبِيلَ الرَّشَادِ (38) يَا قَوْمِ إِنَّمَا هَٰذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا مَتَاعٌ وَإِنَّ الْآخِرَةَ هِيَ دَارُ الْقَرَارِ (39) مَنْ عَمِلَ سَيِّئَةً فَلَا يُجْزَىٰ إِلَّا مِثْلَهَا ۖ وَمَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُولَٰئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ يُرْزَقُونَ فِيهَا بِغَيْرِ حِسَابٍ (40)
الصفحة Page 471
(34) "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka."
(35) "Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa."
(36) Kuma Fir'auna ye ce, "Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi."
(37) "¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra."
(38) Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa."
(39) "Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata."
(40) "Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022