(12) Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.
(13) Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.
(14) Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
(15) Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
(16) Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
(17) Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
(18) Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
(19) Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
(20) Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
(21) Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
(22) Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
(23) Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
(24) Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
(25) "Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."