(44) Gaisuwarsu a rãnar da suke haɗuwa da shi "Salãm", kuma Yã yi musu tattalin wani sakamako na karimci.
(45) Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.
(46) Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa.
(47) Kuma ka yi bushãra ga mũminai cẽwa, sũnã da falalamai girma daga Allah.
(48) Kuma kada ka yi ɗã'a ga kãfirai da munãfukai, kuma ka ƙyã1e cũtarsu (gare ka), kuma ka dõgara ga Allah. Allah Yã isa zama wakĩli.
(49) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi kuma ku sake su saki mai kyau.
(50) Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da 'yã'yan baffanka, da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka, banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.