(48) Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.
(49) Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."
(50) To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.
(51) Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"
(52) "Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?
(53) "To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"
(54) Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
(55) Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
(56) Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.
(57) Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.
(58) Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
(59) Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.
(60) Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa