الرعد   سورة  : Ar-Ra'd


سورة Sura   الرعد   Ar-Ra'd
لَهُ دَعْوَةُ الْحَقِّ ۖ وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِ لَا يَسْتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيْءٍ إِلَّا كَبَاسِطِ كَفَّيْهِ إِلَى الْمَاءِ لِيَبْلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَالِغِهِ ۚ وَمَا دُعَاءُ الْكَافِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَالٍ (14) وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ طَوْعًا وَكَرْهًا وَظِلَالُهُم بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ ۩ (15) قُلْ مَن رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ قُلِ اللَّهُ ۚ قُلْ أَفَاتَّخَذْتُم مِّن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ لَا يَمْلِكُونَ لِأَنفُسِهِمْ نَفْعًا وَلَا ضَرًّا ۚ قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الْأَعْمَىٰ وَالْبَصِيرُ أَمْ هَلْ تَسْتَوِي الظُّلُمَاتُ وَالنُّورُ ۗ أَمْ جَعَلُوا لِلَّهِ شُرَكَاءَ خَلَقُوا كَخَلْقِهِ فَتَشَابَهَ الْخَلْقُ عَلَيْهِمْ ۚ قُلِ اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ وَهُوَ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ (16) أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَسَالَتْ أَوْدِيَةٌ بِقَدَرِهَا فَاحْتَمَلَ السَّيْلُ زَبَدًا رَّابِيًا ۚ وَمِمَّا يُوقِدُونَ عَلَيْهِ فِي النَّارِ ابْتِغَاءَ حِلْيَةٍ أَوْ مَتَاعٍ زَبَدٌ مِّثْلُهُ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ اللَّهُ الْحَقَّ وَالْبَاطِلَ ۚ فَأَمَّا الزَّبَدُ فَيَذْهَبُ جُفَاءً ۖ وَأَمَّا مَا يَنفَعُ النَّاسَ فَيَمْكُثُ فِي الْأَرْضِ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ اللَّهُ الْأَمْثَالَ (17) لِلَّذِينَ اسْتَجَابُوا لِرَبِّهِمُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَالَّذِينَ لَمْ يَسْتَجِيبُوا لَهُ لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُ مَعَهُ لَافْتَدَوْا بِهِ ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ سُوءُ الْحِسَابِ وَمَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ الْمِهَادُ (18)
الصفحة Page 251
(14) Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama ba fãce yanã a cikin ɓata.
(15) Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice.
(16) Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah". Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?" Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi."
(17) Ya saukar da ruwa daga sama, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.
(18) Ga waɗanda suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022