(19) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su ne'yan Jahĩm.
(20) Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai.
(21) Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma.
(22) Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.
(23) Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari.
(24) Watau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde.