الذاريات   سورة  : Adh-Dhaariyat


سورة Sura   الذاريات   Adh-Dhaariyat
كَذَٰلِكَ مَا أَتَى الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ (52) أَتَوَاصَوْا بِهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ (53) فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَا أَنتَ بِمَلُومٍ (54) وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ (55) وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ (56) مَا أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَا أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِ (57) إِنَّ اللَّهَ هُوَ الرَّزَّاقُ ذُو الْقُوَّةِ الْمَتِينُ (58) فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَابِهِمْ فَلَا يَسْتَعْجِلُونِ (59) فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن يَوْمِهِمُ الَّذِي يُوعَدُونَ (60)
الطور At-Tur
وَالطُّورِ (1) وَكِتَابٍ مَّسْطُورٍ (2) فِي رَقٍّ مَّنشُورٍ (3) وَالْبَيْتِ الْمَعْمُورِ (4) وَالسَّقْفِ الْمَرْفُوعِ (5) وَالْبَحْرِ الْمَسْجُورِ (6) إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَاقِعٌ (7) مَّا لَهُ مِن دَافِعٍ (8) يَوْمَ تَمُورُ السَّمَاءُ مَوْرًا (9) وَتَسِيرُ الْجِبَالُ سَيْرًا (10) فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (11) الَّذِينَ هُمْ فِي خَوْضٍ يَلْعَبُونَ (12) يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا (13) هَٰذِهِ النَّارُ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ (14)
الصفحة Page 523
(52) Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
(53) shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
(54) Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
(55) Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
(56) Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
(57) Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
(58) Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
(59) To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
(60) Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
الطور At-Tur
(1) Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).
(2) Da wani littãfi rubũtacce.
(3) A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
(4) Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
(5) Da rufin nan da aka ɗaukaka.
(6) Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
(7) Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
(8) Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
(9) Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
(10) Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
(11) To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
(12) Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
(13) Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
(14) (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022