النساء   سورة  : An-Nisaa


سورة Sura   النساء   An-Nisaa
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَن يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا (60) وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَىٰ مَا أَنزَلَ اللَّهُ وَإِلَى الرَّسُولِ رَأَيْتَ الْمُنَافِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودًا (61) فَكَيْفَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ثُمَّ جَاءُوكَ يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ إِنْ أَرَدْنَا إِلَّا إِحْسَانًا وَتَوْفِيقًا (62) أُولَٰئِكَ الَّذِينَ يَعْلَمُ اللَّهُ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ وَعِظْهُمْ وَقُل لَّهُمْ فِي أَنفُسِهِمْ قَوْلًا بَلِيغًا (63) وَمَا أَرْسَلْنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذ ظَّلَمُوا أَنفُسَهُمْ جَاءُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّابًا رَّحِيمًا (64) فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنفُسِهِمْ حَرَجًا مِّمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا (65)
الصفحة Page 88
(60) Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ¦ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
(61) Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
(62) To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."?
(63) Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
(64) Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.
(65) To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022