(26) "Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
(27) Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
(28) "Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
(29) Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
(30) Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
(31) "Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
(32) "Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
(33) "Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
(34) Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
(35) Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
(36) "Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
(37) Sai ƙungiyõyin suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
(38) Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.