(21) Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.
(22) A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe mu!"
(23) Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya.
(24) Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla.
(25) Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa.
(26) Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani.
(27) Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!
(28) "Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!
(29) "Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.
(30) Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa!"
(31) Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.
(32) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.