(45) Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyinSa.
يس Yaseen
(1) Y. S̃.
(2) Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima.
(3) Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.
(4) A kan hanya madaidaiciya.
(5) (Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
(6) Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.
(7) Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
(8) Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.
(9) Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.
(10) Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.
(11) Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.
(12) Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.