هود   سورة  : Hud


سورة Sura   هود   Hud
يَقْدُمُ قَوْمَهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَأَوْرَدَهُمُ النَّارَ ۖ وَبِئْسَ الْوِرْدُ الْمَوْرُودُ (98) وَأُتْبِعُوا فِي هَٰذِهِ لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ بِئْسَ الرِّفْدُ الْمَرْفُودُ (99) ذَٰلِكَ مِنْ أَنبَاءِ الْقُرَىٰ نَقُصُّهُ عَلَيْكَ ۖ مِنْهَا قَائِمٌ وَحَصِيدٌ (100) وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَٰكِن ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ ۖ فَمَا أَغْنَتْ عَنْهُمْ آلِهَتُهُمُ الَّتِي يَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ مِن شَيْءٍ لَّمَّا جَاءَ أَمْرُ رَبِّكَ ۖ وَمَا زَادُوهُمْ غَيْرَ تَتْبِيبٍ (101) وَكَذَٰلِكَ أَخْذُ رَبِّكَ إِذَا أَخَذَ الْقُرَىٰ وَهِيَ ظَالِمَةٌ ۚ إِنَّ أَخْذَهُ أَلِيمٌ شَدِيدٌ (102) إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّمَنْ خَافَ عَذَابَ الْآخِرَةِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمٌ مَّجْمُوعٌ لَّهُ النَّاسُ وَذَٰلِكَ يَوْمٌ مَّشْهُودٌ (103) وَمَا نُؤَخِّرُهُ إِلَّا لِأَجَلٍ مَّعْدُودٍ (104) يَوْمَ يَأْتِ لَا تَكَلَّمُ نَفْسٌ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ فَمِنْهُمْ شَقِيٌّ وَسَعِيدٌ (105) فَأَمَّا الَّذِينَ شَقُوا فَفِي النَّارِ لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَشَهِيقٌ (106) خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ إِلَّا مَا شَاءَ رَبُّكَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ (107) ۞ وَأَمَّا الَّذِينَ سُعِدُوا فَفِي الْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ إِلَّا مَا شَاءَ رَبُّكَ ۖ عَطَاءً غَيْرَ مَجْذُوذٍ (108)
الصفحة Page 233
(98) Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu.
(99) Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar da ake yi musu.
(100) Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.
(101) Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra.
(102) Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.
(103) Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
(104) Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye.
(105) Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki.
(106) To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta.
(107) Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.
(108) Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022