(30) Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita."
(31) "Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta.
(32) "A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai."
(33) Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?"
(34) Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi.
(35) Kuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima.
(36) Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani.
(37) Kuma akwai daga ãyõyinSa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa.
(38) To, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa.