البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي جَاعِلٌ فِي الْأَرْضِ خَلِيفَةً ۖ قَالُوا أَتَجْعَلُ فِيهَا مَن يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ الدِّمَاءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ ۖ قَالَ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لَا تَعْلَمُونَ (30) وَعَلَّمَ آدَمَ الْأَسْمَاءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى الْمَلَائِكَةِ فَقَالَ أَنبِئُونِي بِأَسْمَاءِ هَٰؤُلَاءِ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (31) قَالُوا سُبْحَانَكَ لَا عِلْمَ لَنَا إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَا ۖ إِنَّكَ أَنتَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ (32) قَالَ يَا آدَمُ أَنبِئْهُم بِأَسْمَائِهِمْ ۖ فَلَمَّا أَنبَأَهُم بِأَسْمَائِهِمْ قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّي أَعْلَمُ غَيْبَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَأَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ (33) وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَىٰ وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ (34) وَقُلْنَا يَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ وَكُلَا مِنْهَا رَغَدًا حَيْثُ شِئْتُمَا وَلَا تَقْرَبَا هَٰذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الظَّالِمِينَ (35) فَأَزَلَّهُمَا الشَّيْطَانُ عَنْهَا فَأَخْرَجَهُمَا مِمَّا كَانَا فِيهِ ۖ وَقُلْنَا اهْبِطُوا بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ وَلَكُمْ فِي الْأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَىٰ حِينٍ (36) فَتَلَقَّىٰ آدَمُ مِن رَّبِّهِ كَلِمَاتٍ فَتَابَ عَلَيْهِ ۚ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ (37)
الصفحة Page 6
(30) Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."
(31) Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."
(32) Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."
(33) Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"
(34) Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
(35) Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."
(36) Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."
(37) Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022