الرحمن   سورة  : Ar-Rahmaan


سورة Sura   الرحمن   Ar-Rahmaan
رَبُّ الْمَشْرِقَيْنِ وَرَبُّ الْمَغْرِبَيْنِ (17) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (18) مَرَجَ الْبَحْرَيْنِ يَلْتَقِيَانِ (19) بَيْنَهُمَا بَرْزَخٌ لَّا يَبْغِيَانِ (20) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (21) يَخْرُجُ مِنْهُمَا اللُّؤْلُؤُ وَالْمَرْجَانُ (22) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (23) وَلَهُ الْجَوَارِ الْمُنشَآتُ فِي الْبَحْرِ كَالْأَعْلَامِ (24) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (25) كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍ (26) وَيَبْقَىٰ وَجْهُ رَبِّكَ ذُو الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ (27) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (28) يَسْأَلُهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ كُلَّ يَوْمٍ هُوَ فِي شَأْنٍ (29) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (30) سَنَفْرُغُ لَكُمْ أَيُّهَ الثَّقَلَانِ (31) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (32) يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ إِنِ اسْتَطَعْتُمْ أَن تَنفُذُوا مِنْ أَقْطَارِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ فَانفُذُوا ۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلْطَانٍ (33) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (34) يُرْسَلُ عَلَيْكُمَا شُوَاظٌ مِّن نَّارٍ وَنُحَاسٌ فَلَا تَنتَصِرَانِ (35) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (36) فَإِذَا انشَقَّتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ وَرْدَةً كَالدِّهَانِ (37) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (38) فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُسْأَلُ عَن ذَنبِهِ إِنسٌ وَلَا جَانٌّ (39) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (40)
الصفحة Page 532
(17) Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
(18) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(19) Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
(20) A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
(21) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(22) Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.
(23) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(24) Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
(25) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(26) Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.
(27) Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
(28) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(29) wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.
(30) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(31) Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!
(32) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(33) Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.
(34) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(35) Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
(36) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(37) Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
(38) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
(39) To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
(40) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022