القصص   سورة  : Al-Qasas


سورة Sura   القصص   Al-Qasas
قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِن جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ اللَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُم بِضِيَاءٍ ۖ أَفَلَا تَسْمَعُونَ (71) قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِن جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ النَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُم بِلَيْلٍ تَسْكُنُونَ فِيهِ ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَ (72) وَمِن رَّحْمَتِهِ جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ لِتَسْكُنُوا فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ (73) وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَائِيَ الَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ (74) وَنَزَعْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا فَقُلْنَا هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ فَعَلِمُوا أَنَّ الْحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ (75) ۞ إِنَّ قَارُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيْهِمْ ۖ وَآتَيْنَاهُ مِنَ الْكُنُوزِ مَا إِنَّ مَفَاتِحَهُ لَتَنُوءُ بِالْعُصْبَةِ أُولِي الْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُ قَوْمُهُ لَا تَفْرَحْ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْفَرِحِينَ (76) وَابْتَغِ فِيمَا آتَاكَ اللَّهُ الدَّارَ الْآخِرَةَ ۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ الدُّنْيَا ۖ وَأَحْسِن كَمَا أَحْسَنَ اللَّهُ إِلَيْكَ ۖ وَلَا تَبْغِ الْفَسَادَ فِي الْأَرْضِ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ (77)
الصفحة Page 394
(71) Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"
(72) Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?"
(73) "Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
(74) Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"
(75) Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
(76) Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."
(77) "Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022