الرعد   سورة  : Ar-Ra'd


سورة Sura   الرعد   Ar-Ra'd
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ الْحَسَنَةِ وَقَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِمُ الْمَثُلَاتُ ۗ وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغْفِرَةٍ لِّلنَّاسِ عَلَىٰ ظُلْمِهِمْ ۖ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ الْعِقَابِ (6) وَيَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ ۗ إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرٌ ۖ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ (7) اللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَحْمِلُ كُلُّ أُنثَىٰ وَمَا تَغِيضُ الْأَرْحَامُ وَمَا تَزْدَادُ ۖ وَكُلُّ شَيْءٍ عِندَهُ بِمِقْدَارٍ (8) عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْكَبِيرُ الْمُتَعَالِ (9) سَوَاءٌ مِّنكُم مَّنْ أَسَرَّ الْقَوْلَ وَمَن جَهَرَ بِهِ وَمَنْ هُوَ مُسْتَخْفٍ بِاللَّيْلِ وَسَارِبٌ بِالنَّهَارِ (10) لَهُ مُعَقِّبَاتٌ مِّن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ يَحْفَظُونَهُ مِنْ أَمْرِ اللَّهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنفُسِهِمْ ۗ وَإِذَا أَرَادَ اللَّهُ بِقَوْمٍ سُوءًا فَلَا مَرَدَّ لَهُ ۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَالٍ (11) هُوَ الَّذِي يُرِيكُمُ الْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنشِئُ السَّحَابَ الثِّقَالَ (12) وَيُسَبِّحُ الرَّعْدُ بِحَمْدِهِ وَالْمَلَائِكَةُ مِنْ خِيفَتِهِ وَيُرْسِلُ الصَّوَاعِقَ فَيُصِيبُ بِهَا مَن يَشَاءُ وَهُمْ يُجَادِلُونَ فِي اللَّهِ وَهُوَ شَدِيدُ الْمِحَالِ (13)
الصفحة Page 250
(6) Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne.
(7) Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijinsa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa.
(8) Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake.
(9) Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki.
(10) Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna.
(11) (Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci baicin Shi.
(12) Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi.
(13) Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022