الأحقاف   سورة  : Al-Ahqaf


سورة Sura   الأحقاف   Al-Ahqaf
وَوَصَّيْنَا الْإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ إِحْسَانًا ۖ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ كُرْهًا وَوَضَعَتْهُ كُرْهًا ۖ وَحَمْلُهُ وَفِصَالُهُ ثَلَاثُونَ شَهْرًا ۚ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَةً قَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَصْلِحْ لِي فِي ذُرِّيَّتِي ۖ إِنِّي تُبْتُ إِلَيْكَ وَإِنِّي مِنَ الْمُسْلِمِينَ (15) أُولَٰئِكَ الَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنْهُمْ أَحْسَنَ مَا عَمِلُوا وَنَتَجَاوَزُ عَن سَيِّئَاتِهِمْ فِي أَصْحَابِ الْجَنَّةِ ۖ وَعْدَ الصِّدْقِ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ (16) وَالَّذِي قَالَ لِوَالِدَيْهِ أُفٍّ لَّكُمَا أَتَعِدَانِنِي أَنْ أُخْرَجَ وَقَدْ خَلَتِ الْقُرُونُ مِن قَبْلِي وَهُمَا يَسْتَغِيثَانِ اللَّهَ وَيْلَكَ آمِنْ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ فَيَقُولُ مَا هَٰذَا إِلَّا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ (17) أُولَٰئِكَ الَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ الْقَوْلُ فِي أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِم مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا خَاسِرِينَ (18) وَلِكُلٍّ دَرَجَاتٌ مِّمَّا عَمِلُوا ۖ وَلِيُوَفِّيَهُمْ أَعْمَالَهُمْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ (19) وَيَوْمَ يُعْرَضُ الَّذِينَ كَفَرُوا عَلَى النَّارِ أَذْهَبْتُمْ طَيِّبَاتِكُمْ فِي حَيَاتِكُمُ الدُّنْيَا وَاسْتَمْتَعْتُم بِهَا فَالْيَوْمَ تُجْزَوْنَ عَذَابَ الْهُونِ بِمَا كُنتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَبِمَا كُنتُمْ تَفْسُقُونَ (20)
الصفحة Page 504
(15) Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."
(16) Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi).
(17) Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
(18) Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.
(19) Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba.
(20) Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022