(12) Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta.
(13) Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can.
(14) Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa.
(15) Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma."
(16) "Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka."
(17) Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"
(18) suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."
(19) To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
(20) Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.