آل عمران   سورة  : Aal-Imran


سورة Sura   آل عمران   Aal-Imran
۞ وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ (133) الَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ (134) وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَن يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَىٰ مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ (135) أُولَٰئِكَ جَزَاؤُهُم مَّغْفِرَةٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَجَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ (136) قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُمْ سُنَنٌ فَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ (137) هَٰذَا بَيَانٌ لِّلنَّاسِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ (138) وَلَا تَهِنُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَنتُمُ الْأَعْلَوْنَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ (139) إِن يَمْسَسْكُمْ قَرْحٌ فَقَدْ مَسَّ الْقَوْمَ قَرْحٌ مِّثْلُهُ ۚ وَتِلْكَ الْأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَيَتَّخِذَ مِنكُمْ شُهَدَاءَ ۗ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ (140)
الصفحة Page 67
(133) Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.
(134) Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
(135) Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane.
(136) Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki.
(137) Lalle ne misãlai sun shũɗe a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin ƙasa sa'an nan ku dũba, yãyã ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
(138) Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiryuwa ce da wa'azi ga mãsu taƙawa.
(139) Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya ɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni.
(140) Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022