البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
۞ لَّيْسَ الْبِرَّ أَن تُوَلُّوا وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَٰكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ وَآتَى الْمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِ ذَوِي الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ وَالسَّائِلِينَ وَفِي الرِّقَابِ وَأَقَامَ الصَّلَاةَ وَآتَى الزَّكَاةَ وَالْمُوفُونَ بِعَهْدِهِمْ إِذَا عَاهَدُوا ۖ وَالصَّابِرِينَ فِي الْبَأْسَاءِ وَالضَّرَّاءِ وَحِينَ الْبَأْسِ ۗ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ صَدَقُوا ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ (177) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِصَاصُ فِي الْقَتْلَى ۖ الْحُرُّ بِالْحُرِّ وَالْعَبْدُ بِالْعَبْدِ وَالْأُنثَىٰ بِالْأُنثَىٰ ۚ فَمَنْ عُفِيَ لَهُ مِنْ أَخِيهِ شَيْءٌ فَاتِّبَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ وَأَدَاءٌ إِلَيْهِ بِإِحْسَانٍ ۗ ذَٰلِكَ تَخْفِيفٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَرَحْمَةٌ ۗ فَمَنِ اعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ (178) وَلَكُمْ فِي الْقِصَاصِ حَيَاةٌ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (179) كُتِبَ عَلَيْكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ إِن تَرَكَ خَيْرًا الْوَصِيَّةُ لِلْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ بِالْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى الْمُتَّقِينَ (180) فَمَن بَدَّلَهُ بَعْدَمَا سَمِعَهُ فَإِنَّمَا إِثْمُهُ عَلَى الَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (181)
الصفحة Page 27
(177) Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.
(178) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.
(179) Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.
(180) Kuma an wajabta, a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.
(181) To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022