الغاشية   سورة  : Al-Ghaashiya


سورة Sura   الغاشية   Al-Ghaashiya
بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (16) وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ (17) إِنَّ هَٰذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَىٰ (18) صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ (19)
الغاشية Al-Ghaashiya
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ (1) وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ (2) عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ (3) تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً (4) تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ (5) لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ (6) لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِن جُوعٍ (7) وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ (8) لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ (9) فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ (10) لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً (11) فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ (12) فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ (13) وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ (14) وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ (15) وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ (16) أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ (17) وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ (18) وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ (19) وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ (20) فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ (21) لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ (22) إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ (23) فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ (24) إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ (25) ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم (26)
الصفحة Page 592
(16) Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
(17) Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
(18) Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
(19) Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
الغاشية Al-Ghaashiya
(1) Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
(2) Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
(3) Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
(4) Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
(5) Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
(6) Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
(7) Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
(8) Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
(9) Game da aikinsu, masu yarda ne.
(10) (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
(11) Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
(12) A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
(13) A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
(14) Da kõfuna ar'aje.
(15) Da filõli jẽre,
(16) Da katifu shimfiɗe.
(17) Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
(18) Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
(19) Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
(20) Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
(21) sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
(22) Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
(23) Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
(24) To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
(25) Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
(26) Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022