(21) Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya.
(22) Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai girma.
(23) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.
(24) Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."
(25) Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.
(26) Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai, kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai.