(10) Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma.
(11) Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa."
(12) Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku.
(13) Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai.
(14) Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
(15) Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan.