ابراهيم   سورة  : Ibrahim


سورة Sura   ابراهيم   Ibrahim
مُهْطِعِينَ مُقْنِعِي رُءُوسِهِمْ لَا يَرْتَدُّ إِلَيْهِمْ طَرْفُهُمْ ۖ وَأَفْئِدَتُهُمْ هَوَاءٌ (43) وَأَنذِرِ النَّاسَ يَوْمَ يَأْتِيهِمُ الْعَذَابُ فَيَقُولُ الَّذِينَ ظَلَمُوا رَبَّنَا أَخِّرْنَا إِلَىٰ أَجَلٍ قَرِيبٍ نُّجِبْ دَعْوَتَكَ وَنَتَّبِعِ الرُّسُلَ ۗ أَوَلَمْ تَكُونُوا أَقْسَمْتُم مِّن قَبْلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٍ (44) وَسَكَنتُمْ فِي مَسَاكِنِ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ وَتَبَيَّنَ لَكُمْ كَيْفَ فَعَلْنَا بِهِمْ وَضَرَبْنَا لَكُمُ الْأَمْثَالَ (45) وَقَدْ مَكَرُوا مَكْرَهُمْ وَعِندَ اللَّهِ مَكْرُهُمْ وَإِن كَانَ مَكْرُهُمْ لِتَزُولَ مِنْهُ الْجِبَالُ (46) فَلَا تَحْسَبَنَّ اللَّهَ مُخْلِفَ وَعْدِهِ رُسُلَهُ ۗ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ ذُو انتِقَامٍ (47) يَوْمَ تُبَدَّلُ الْأَرْضُ غَيْرَ الْأَرْضِ وَالسَّمَاوَاتُ ۖ وَبَرَزُوا لِلَّهِ الْوَاحِدِ الْقَهَّارِ (48) وَتَرَى الْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذٍ مُّقَرَّنِينَ فِي الْأَصْفَادِ (49) سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٍ وَتَغْشَىٰ وُجُوهَهُمُ النَّارُ (50) لِيَجْزِيَ اللَّهُ كُلَّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ (51) هَٰذَا بَلَاغٌ لِّلنَّاسِ وَلِيُنذَرُوا بِهِ وَلِيَعْلَمُوا أَنَّمَا هُوَ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ وَلِيَذَّكَّرَ أُولُو الْأَلْبَابِ (52)
الصفحة Page 261
(43) "Sunã mãsu gaggãwa, mãsu ɗaukaka kãwunansu zuwa sama ƙiftawar ganinsu ba ta kõmãwa gare su. Kuma zukãtansu wõfintattu."
(44) Kuma ka yi gargaɗi ga mutãne ga rãnar da azãba take jẽ musu, sai waɗanda suka yi zãlunci su ce: "Yã Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwã ba daga gabãni, cẽwa bã ku da wata gushẽwa?
(45) "Kuma kuka zaunã a cikin gidãjen waɗanda suka zãlunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikatã game da su, kuma Muka buga muku misãlai."
(46) Kuma lalle sun yi mãkirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu yã kasance, haƙĩƙa, duwãtsu sunã gushẽwã sabõda shi.
(47) Sabõda haka, kada ka ƙarfafa zaton Allah Mai sãɓa wa'adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwãyi, Ma'abũcin azãbar rãmuwa.
(48) A rãnar da ake musanya ƙasa bã ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasãwa.
(49) Kuma kana ganin mãsu laifi, a rãnar nan, sunã waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin marũruwa.
(50) Rigunansu daga farar wutã ne, kuma wuta ta rufe fuskõkinsu.
(51) Dõmin Allah Ya sãkã wa kõwane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggãwar hisãbi ne.
(52) Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su riƙa tunãwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022