الكهف   سورة  : Al-Kahf


سورة Sura   الكهف   Al-Kahf
وَدَخَلَ جَنَّتَهُ وَهُوَ ظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ قَالَ مَا أَظُنُّ أَن تَبِيدَ هَٰذِهِ أَبَدًا (35) وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِن رُّدِدتُّ إِلَىٰ رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيْرًا مِّنْهَا مُنقَلَبًا (36) قَالَ لَهُ صَاحِبُهُ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَكَفَرْتَ بِالَّذِي خَلَقَكَ مِن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ سَوَّاكَ رَجُلًا (37) لَّٰكِنَّا هُوَ اللَّهُ رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِرَبِّي أَحَدًا (38) وَلَوْلَا إِذْ دَخَلْتَ جَنَّتَكَ قُلْتَ مَا شَاءَ اللَّهُ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ ۚ إِن تَرَنِ أَنَا أَقَلَّ مِنكَ مَالًا وَوَلَدًا (39) فَعَسَىٰ رَبِّي أَن يُؤْتِيَنِ خَيْرًا مِّن جَنَّتِكَ وَيُرْسِلَ عَلَيْهَا حُسْبَانًا مِّنَ السَّمَاءِ فَتُصْبِحَ صَعِيدًا زَلَقًا (40) أَوْ يُصْبِحَ مَاؤُهَا غَوْرًا فَلَن تَسْتَطِيعَ لَهُ طَلَبًا (41) وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِ فَأَصْبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيْهِ عَلَىٰ مَا أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُشْرِكْ بِرَبِّي أَحَدًا (42) وَلَمْ تَكُن لَّهُ فِئَةٌ يَنصُرُونَهُ مِن دُونِ اللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِرًا (43) هُنَالِكَ الْوَلَايَةُ لِلَّهِ الْحَقِّ ۚ هُوَ خَيْرٌ ثَوَابًا وَخَيْرٌ عُقْبًا (44) وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاءٍ أَنزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الْأَرْضِ فَأَصْبَحَ هَشِيمًا تَذْرُوهُ الرِّيَاحُ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ مُّقْتَدِرًا (45)
الصفحة Page 298
(35) Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada."
(36) "Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma."
(37) Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"
(38) "Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba"
(39) "Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."
(40) "To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi."
(41) "Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta."
(42) Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"
(43) Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba.
(44) A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kumaMafĩ fĩci ga ãƙiba.
(45) Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022