الحج   سورة  : Al-Hajj


سورة Sura   الحج   Al-Hajj
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَاهُ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ وَأَنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَن يُرِيدُ (16) إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئِينَ وَالنَّصَارَىٰ وَالْمَجُوسَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا إِنَّ اللَّهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ (17) أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يَسْجُدُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ وَالنُّجُومُ وَالْجِبَالُ وَالشَّجَرُ وَالدَّوَابُّ وَكَثِيرٌ مِّنَ النَّاسِ ۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيْهِ الْعَذَابُ ۗ وَمَن يُهِنِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِن مُّكْرِمٍ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ ۩ (18) ۞ هَٰذَانِ خَصْمَانِ اخْتَصَمُوا فِي رَبِّهِمْ ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا قُطِّعَتْ لَهُمْ ثِيَابٌ مِّن نَّارٍ يُصَبُّ مِن فَوْقِ رُءُوسِهِمُ الْحَمِيمُ (19) يُصْهَرُ بِهِ مَا فِي بُطُونِهِمْ وَالْجُلُودُ (20) وَلَهُم مَّقَامِعُ مِنْ حَدِيدٍ (21) كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا مِنْ غَمٍّ أُعِيدُوا فِيهَا وَذُوقُوا عَذَابَ الْحَرِيقِ (22) إِنَّ اللَّهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَلُؤْلُؤًا ۖ وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِيرٌ (23)
الصفحة Page 334
(16) Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi.
(17) Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme.
(18) Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so.
(19) waɗannan ƙungiyõyi biyu ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.
(20) Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu.
(21) Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe.
(22) A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azãbar gõbara."
(23) Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022