المؤمنون   سورة  : Al-Muminoon


سورة Sura   المؤمنون   Al-Muminoon
وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً بِقَدَرٍ فَأَسْكَنَّاهُ فِي الْأَرْضِ ۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابٍ بِهِ لَقَادِرُونَ (18) فَأَنشَأْنَا لَكُم بِهِ جَنَّاتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ لَّكُمْ فِيهَا فَوَاكِهُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ (19) وَشَجَرَةً تَخْرُجُ مِن طُورِ سَيْنَاءَ تَنبُتُ بِالدُّهْنِ وَصِبْغٍ لِّلْآكِلِينَ (20) وَإِنَّ لَكُمْ فِي الْأَنْعَامِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهَا وَلَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ (21) وَعَلَيْهَا وَعَلَى الْفُلْكِ تُحْمَلُونَ (22) وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ (23) فَقَالَ الْمَلَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ مَا هَٰذَا إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيْكُمْ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَأَنزَلَ مَلَائِكَةً مَّا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِي آبَائِنَا الْأَوَّلِينَ (24) إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ بِهِ جِنَّةٌ فَتَرَبَّصُوا بِهِ حَتَّىٰ حِينٍ (25) قَالَ رَبِّ انصُرْنِي بِمَا كَذَّبُونِ (26) فَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِ أَنِ اصْنَعِ الْفُلْكَ بِأَعْيُنِنَا وَوَحْيِنَا فَإِذَا جَاءَ أَمْرُنَا وَفَارَ التَّنُّورُ ۙ فَاسْلُكْ فِيهَا مِن كُلٍّ زَوْجَيْنِ اثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيْهِ الْقَوْلُ مِنْهُمْ ۖ وَلَا تُخَاطِبْنِي فِي الَّذِينَ ظَلَمُوا ۖ إِنَّهُم مُّغْرَقُونَ (27)
الصفحة Page 343
(18) Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.
(19) Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
(20) Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
(21) Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
(22) Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
(23) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?"
(24) Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko."
(25) "Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci."
(26) Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani."
(27) Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022