النور   سورة  : An-Noor


سورة Sura   النور   An-Noor
إِنَّ الَّذِينَ جَاءُوا بِالْإِفْكِ عُصْبَةٌ مِّنكُمْ ۚ لَا تَحْسَبُوهُ شَرًّا لَّكُم ۖ بَلْ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۚ لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُم مَّا اكْتَسَبَ مِنَ الْإِثْمِ ۚ وَالَّذِي تَوَلَّىٰ كِبْرَهُ مِنْهُمْ لَهُ عَذَابٌ عَظِيمٌ (11) لَّوْلَا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ ظَنَّ الْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بِأَنفُسِهِمْ خَيْرًا وَقَالُوا هَٰذَا إِفْكٌ مُّبِينٌ (12) لَّوْلَا جَاءُوا عَلَيْهِ بِأَرْبَعَةِ شُهَدَاءَ ۚ فَإِذْ لَمْ يَأْتُوا بِالشُّهَدَاءِ فَأُولَٰئِكَ عِندَ اللَّهِ هُمُ الْكَاذِبُونَ (13) وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ لَمَسَّكُمْ فِي مَا أَفَضْتُمْ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ (14) إِذْ تَلَقَّوْنَهُ بِأَلْسِنَتِكُمْ وَتَقُولُونَ بِأَفْوَاهِكُم مَّا لَيْسَ لَكُم بِهِ عِلْمٌ وَتَحْسَبُونَهُ هَيِّنًا وَهُوَ عِندَ اللَّهِ عَظِيمٌ (15) وَلَوْلَا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ قُلْتُم مَّا يَكُونُ لَنَا أَن نَّتَكَلَّمَ بِهَٰذَا سُبْحَانَكَ هَٰذَا بُهْتَانٌ عَظِيمٌ (16) يَعِظُكُمُ اللَّهُ أَن تَعُودُوا لِمِثْلِهِ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ (17) وَيُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمُ الْآيَاتِ ۚ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ (18) إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۚ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ (19) وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ وَأَنَّ اللَّهَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ (20)
الصفحة Page 351
(11) Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.
(12) Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"
(13) Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.
(14) Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.
(15) A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.
(16) Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"?
(17) Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai.
(18) Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
(19) Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.
(20) Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022