آل عمران   سورة  : Aal-Imran


سورة Sura   آل عمران   Aal-Imran
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَن تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلَا أَوْلَادُهُم مِّنَ اللَّهِ شَيْئًا ۖ وَأُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۚ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ (116) مَثَلُ مَا يُنفِقُونَ فِي هَٰذِهِ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَثَلِ رِيحٍ فِيهَا صِرٌّ أَصَابَتْ حَرْثَ قَوْمٍ ظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ فَأَهْلَكَتْهُ ۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ اللَّهُ وَلَٰكِنْ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ (117) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا بِطَانَةً مِّن دُونِكُمْ لَا يَأْلُونَكُمْ خَبَالًا وَدُّوا مَا عَنِتُّمْ قَدْ بَدَتِ الْبَغْضَاءُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ وَمَا تُخْفِي صُدُورُهُمْ أَكْبَرُ ۚ قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ الْآيَاتِ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ (118) هَا أَنتُمْ أُولَاءِ تُحِبُّونَهُمْ وَلَا يُحِبُّونَكُمْ وَتُؤْمِنُونَ بِالْكِتَابِ كُلِّهِ وَإِذَا لَقُوكُمْ قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا عَضُّوا عَلَيْكُمُ الْأَنَامِلَ مِنَ الْغَيْظِ ۚ قُلْ مُوتُوا بِغَيْظِكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ (119) إِن تَمْسَسْكُمْ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ وَإِن تُصِبْكُمْ سَيِّئَةٌ يَفْرَحُوا بِهَا ۖ وَإِن تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا لَا يَضُرُّكُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا ۗ إِنَّ اللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ (120) وَإِذْ غَدَوْتَ مِنْ أَهْلِكَ تُبَوِّئُ الْمُؤْمِنِينَ مَقَاعِدَ لِلْقِتَالِ ۗ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (121)
الصفحة Page 65
(116) Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.
(117) Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
(118) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
(119) Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
(120) Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne.
(121) Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022