لقمان   سورة  : Luqman


سورة Sura   لقمان   Luqman
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِي إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى وَأَنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (29) ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ (30) أَلَمْ تَرَ أَنَّ الْفُلْكَ تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِنِعْمَتِ اللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنْ آيَاتِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ (31) وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوْجٌ كَالظُّلَلِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ فَمِنْهُم مُّقْتَصِدٌ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلَّا كُلُّ خَتَّارٍ كَفُورٍ (32) يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ وَاخْشَوْا يَوْمًا لَّا يَجْزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِ وَلَا مَوْلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِ شَيْئًا ۚ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ ۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِاللَّهِ الْغَرُورُ (33) إِنَّ اللَّهَ عِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ الْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْأَرْحَامِ ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ مَّاذَا تَكْسِبُ غَدًا ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ بِأَيِّ أَرْضٍ تَمُوتُ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ (34)
الصفحة Page 414
(29) Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?
(30) Wannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, A1lah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.
(31) Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya.
(32) Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci.
(33) Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin nan ya rũɗẽ ku game da Allah.
(34) Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022