النساء   سورة  : An-Nisaa


سورة Sura   النساء   An-Nisaa
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَعَنَهُمُ اللَّهُ ۖ وَمَن يَلْعَنِ اللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُ نَصِيرًا (52) أَمْ لَهُمْ نَصِيبٌ مِّنَ الْمُلْكِ فَإِذًا لَّا يُؤْتُونَ النَّاسَ نَقِيرًا (53) أَمْ يَحْسُدُونَ النَّاسَ عَلَىٰ مَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ ۖ فَقَدْ آتَيْنَا آلَ إِبْرَاهِيمَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَآتَيْنَاهُم مُّلْكًا عَظِيمًا (54) فَمِنْهُم مَّنْ آمَنَ بِهِ وَمِنْهُم مَّن صَدَّ عَنْهُ ۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ سَعِيرًا (55) إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا سَوْفَ نُصْلِيهِمْ نَارًا كُلَّمَا نَضِجَتْ جُلُودُهُم بَدَّلْنَاهُمْ جُلُودًا غَيْرَهَا لِيَذُوقُوا الْعَذَابَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمًا (56) وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَنُدْخِلُهُمْ ظِلًّا ظَلِيلًا (57) ۞ إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَىٰ أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُم بَيْنَ النَّاسِ أَن تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ ۚ إِنَّ اللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ سَمِيعًا بَصِيرًا (58) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا (59)
الصفحة Page 87
(52) Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.
(53) Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.
(54) Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
(55) To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.
(56) Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
(57) Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
(58) Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.
(59) Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022