الشورى   سورة  : Ash-Shura


سورة Sura   الشورى   Ash-Shura
الشورى Ash-Shura
حم (1) عسق (2) كَذَٰلِكَ يُوحِي إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (3) لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ (4) تَكَادُ السَّمَاوَاتُ يَتَفَطَّرْنَ مِن فَوْقِهِنَّ ۚ وَالْمَلَائِكَةُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِمَن فِي الْأَرْضِ ۗ أَلَا إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ (5) وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ اللَّهُ حَفِيظٌ عَلَيْهِمْ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍ (6) وَكَذَٰلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لِّتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَىٰ وَمَنْ حَوْلَهَا وَتُنذِرَ يَوْمَ الْجَمْعِ لَا رَيْبَ فِيهِ ۚ فَرِيقٌ فِي الْجَنَّةِ وَفَرِيقٌ فِي السَّعِيرِ (7) وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَهُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن يُدْخِلُ مَن يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ ۚ وَالظَّالِمُونَ مَا لَهُم مِّن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ (8) أَمِ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۖ فَاللَّهُ هُوَ الْوَلِيُّ وَهُوَ يُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ (9) وَمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ مِن شَيْءٍ فَحُكْمُهُ إِلَى اللَّهِ ۚ ذَٰلِكُمُ اللَّهُ رَبِّي عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُ (10)
الصفحة Page 483
الشورى Ash-Shura
(1) Ḥ. M̃.
(2) Ĩ. Ṣ̃.
(3) Kamar wancãn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka.
(4) (Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
(5) Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
(6) Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.
(7) Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.
(8) Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki.
(9) Kõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme.
(10) Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022